Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Su dai jamiyun suna zargin gwamnatin kasar da kokarin jan kafa a kalandar da aka tsara ta jadawalin mika mulki a kasar, da za’ayi a watan Fabarerun shekara ta 2022
Idan ana iya tunawa a baya bayan nan ne kungiyar tarayyar Afrika da ta bunkasa tattalin arzikin Afrika Ecowas suka aike da tawaga zuwa birnin Bamako domin matsin lamba kan gwamnatin kasar da ta yi aiki da Alkawarin da ta dauka na shirya zabe a lokacin da aka tsara. Sai dai fira ministan Choguel Miaga ya sansar da cewa akwai yi yuwar a samu jinkiri na yan watanni kafin mika mulki.
A yau ne shuwagabannin kasashen Afrika suke gudanar da taro kan halin da kasashen Mali da Guinea ke ciki domin gano bakin zaren warware matsalar kasashen da taki ci taki cinyewa.
342/